A Visionary Leader in Health and Public Service

Teacher Uban Karatu; Iya Ingancinka Iya Ingancin Al’umma!

0 14

By Dr Nuruddeen Muhammad

Yau ta ke ranar malamai ta duniya.

A wannan rana a fadin duniya ake gudanar da bikin zagayowar Ranar Malamai ta Duniya.

Rana ce ta musamman da Majalisar D’inkin Duniya (UN) ta ware domin tunawa da ranar da hukumarta ta Harkar Ilmi, Kimiyya da kuma Al’adu (UNESCO), da kuma K’ungiyar K’wadago Ta K’asa Da K’asa (ILO) su ka rattaba hannu akan wani daftari a kan daraja, inganci da kuma yanayi da halin da malamai da kuma ita kanta harkar koyarwar ke ciki a duniya baki daya.

Kamata ya yi a ce wannan rana ta kasance wani lokaci ne na yin karatun ta nutsu, musamman a nan k’asarmu Najeriya, inda a sama da shekara arba’in kullum inganci da kuma darajar malamai da aikin koyarwa suke ci gaba da ta6ar6arewa, inda a yanzu haka lamarin ya wuce a kirashi da abin takaici, sai dai na ban tsoro da tashin hankali!

Malamai dai sune ginshik’in al’umma, kuma sune ke rik’e da madafun ikon d’ora al’ummar gaba d’ayanta a turbar ilminta, addininta, wayewarta, da’arta, k’arfin tattalin arzik’inta, lafiyarta, tsaronta, da kuma walwalarta. A tak’aice dai za a iya cewa, iya igancin malamai, iya ingancin al’ummar da suke cikinta. Wato dai, malamai sune ruhi ko jigon al’umma don cigabanta da kuma samun nasararta a tsakanin sauran al’ummomi da ke wannan duniya ta subhana.

Tarihi ya nuna cewa babu wata al’umma ko kuma k’asa da ta fatattaki talauci, halin rashin tsaro, yunwa da kuma cututtuka face sai da wannan al’umma ta fara da sanin daraja, martabawa tare da inganta rayuwa da yanayin aikin malamanta.

Duk irin dambarwar da ke gudana a wannan k’asa ta fannin cigaba, da kuma kwan-gaba-kwan-baya da a ke fama wadda a kullum ta ke nuna mana cewa jiya tafi yau, to ba komai ne ya haddasa hakan ba, illa rik’on sakainar kashi da kuma nuna halin ko-in-kula da al’umma da muhukuntan cikinta su ke ci gaba da yi a kan muhimmancin bangaren ilimi da kuma ingancin su kan su malaman.

Don haka, ya zama dole mu tashi tsaye, a matsayinmu na d’aid’aiku da kuma a gwamnatance, domin bada muhimmanci da kuma tabbbatar da an inganta tsari da rayuwar mutanen da mu ke tara mu su ‘ya’yanmu domin su mai da su cikakkun mutane. Ma’ana dai, mu baiwa malamai daraja kamar yadda suka cancanta.

Shi kuwa malami darajarsa ba ta wuce a ce an saka shi a cikin layin ma’aikatan da su ka fi kowa girman albashi da romon aiki ba. Ingancinsa kuwa ba ya wuce a ce duk wani mai rik’e alli ya iya ta6a allin!

Dabara dai an ce ta rage ga mai shiga rijiya; dole dai sai al’umma ta mike tsaye wajen nemawa kan ta mafita!

Comments
Loading...