A Visionary Leader in Health and Public Service

Sara da Duba Bakin Gatari: Darussa a kan Mulki, Siyasa, Biyayya, da Gwagwarmayar K’arin Gogewa

0 6

Sara da Duba Bakin Gatari: Darussa a kan Mulki, Siyasa, Biyayya, da Gwagwarmayar K’arin Gogewa.

Daga Dr Nuruddeen Muhammad

Shekaru goma da suka gabata ne dai a rana irin ta yau, 28 ga watan Junairu, 2015 na yi wa shugaban k’asa Dr Goodluck Ebele Jonathan sallama ta k’arshe bayan sauk’a daga mukamaina na minista a ma’aikatu guda biyu; K’aramin Ministan Harkokin K’asashen Waje da kuma Minista Mai Sa Ido Kan Ma’aikatar Yad’a Labarai Ta Tarayyar Najeriya. Daga k’arshe dai shugaban ya sahalemin tafiya bayan wata musayar wasik’u da aka yi tsakanin fadar gwamnatin Jigawa da ke Dutse, wanda babana kuma jigona a siyasa ya sanya hannu, wato gwamnan jihar Jigawa na wancan lokacin, Alhaji Sule Lamido, da kuma shi kansa mai kasar, Dr Goodluck Jonathan. Wannan dai shine ya kawo k’arshen wannan aiki na shekara uku da rabi da na fara ranar 14 ga watan Yuli, na shekarar 2011.

A wannann waiwaye da zan yi, zan yi tsokaci a kan wasu 6oyayyun lamura, da muradai, da kuma sark’ak’iyar da ke tattare da wannan bulaguro na shekara goma, da kuma nuni a kan muhimmancin biyayya da rik’e amana, da kuma juriya da duk abun da rik’on amanar kan iya jawo ma ka, sannan kuma daga baya na d’an yi tsokaci a kan buk’atar ci gaba da gwagwarmaya domin k’ara gogewa da kuma dogaro da kai a tsakanin y’an siyasar mu, musammam matasa a cikinsu. Domin akwai bayyanannun misalai da ke nuni da cewa matasa da yawa irina da su ka kai k’ololuwa irin ta mulki da wuri kan iya fama da yadda za su ci gaba da rayuwa bayan k’arewar mulkin. Fata na shine wannan rubutu ya zama kamar madubi a gun matasa da ke rik’e da madafun iko a yanzu, harma da wad’anda Allah SWT zai kawo nan gaba.

Duk da cewa Shugaba Jonathan da Gwamna Lamido sun yi min sani na gaske, kuma suna da k’warin gwiwar cewa da alama dai giyar mulkin ba ta shige ni ba, amma duk da haka ina zargin cewa su na jin wani nauyi a wuyan su na tabbatar da cewa rayuwa na bai rasa madafa bayan na bar mulki ba; da siyasa ko babu siyasa. Dukansu biyun su na da wani tunani da kyakkywan hange a kaina a inda, a cewar su biyun a lokuta daban-daban kuma sau da yawa, zan zama mai matukar amfani ga al’ummar da zan kasance da su (ya dangata da ma’anar da ka baiwa hakan). Nauyi na wannan k’yak’yawan zato na su da kuma abubuwan da duka biyun su ka tsara a kaina ya sa na zubawa kai na ido na k’urulla a madubin wayar da ke hannuna a yayin da jerin gwanon motoci na ke futowa daga fadar gwamnatin tarayya ta Aso Rock a wannan rana (a sanadiyyar hakan na dauki wannan hoton dake mak’ale da wannan rubutun).

A yayin da Shugaba Jonathan ya d’aura niyyar dawo da ni (tare da wa su matasa masu yawa kamar yadda ya tabbatar min) a matsayin babban ministan harkokin kasashen waje a gwamnatinsa, a wa’adinsa na biyu, shi kuwa Baba Lamido, a gurinsa har goben ta yi, ta na nan kuma akan doron abin da ya fi sani fiye da komai a duniya; siyasar zabe da takara. Ina dan shekaru 37 na dawo gida domin tsayawa takarar mataimakin gwamna, tare da Mallam Aminu Ibrahim Ringim, wanda a lokacin ya kasance dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a kakar zaben 2015 a jihar Jigawa.

Toh amma ni ma fa ina da d’inbin tsare-tsare na k’ashin kai na. Babban abin da na fi sha’awa na yi a wannan lokacin shi ne in ƙarfafa sabuwar ƙwarewar da na samu da gogewa a duniya ta hanyar karatun Tsare-Tsare na Al’umma Da Kuma Gudanarwar Mulki (wato Public Policy and Administration) a Tsangayar Harvard Kennedy Ta Jami’ar Harvard, a ƙasar Amurka. Zan dawo kan wannan batun daga baya.

Sai dai ina kyautata zaton cewa Gwamna Sule Lamido ya na so ya karkata akalar manyan manyan digirina a fannin likitanci da sabbin fasahohi da kwarewa da gogewa da na samo a fannin sarrafa k’asa da tsaronta, diflomasiyya, huldar k’asa da k’asa, da siyasar duniya da kuma gudanar da ita, su fuskanci zahirin yanayi irin na mu na k’aramin zama a karkara, da y’an kunji-kunjin mu, da kuma d’inbun k’alubalen da ke gaban mu. A tunanin sa, wadda kuma tabbas hakane, matsawar ba a kafa min turke mai k’arfi a gida ba, to fah tabbas zan sulale ne kawai na shiga cikin hada-hadar duniya. Hakan kuma, a tunanina, ni ma ba dole ya kasance laifi na ba ne a wannan lokacin. Domin k’arfin tasirin shekaru kusan ashirin a jere na karatu mai chanja mutum irin na likitanci mai zurfi, da kuma bud’e ido da gogayya a k’oluluwar k’asa da kuma duniya a kuma yanayi irin na k’uruciya kan iya juya k’wak’walwar mutane da yawa ballantana kuma matashi.

A karshe dai tikitin mu ya sha kaye a Jigawa. Kamar dai yadda ta kasance a sauran jihohin Arewa ma su yawa, sanadiyyar tasirin dad’in bakin General Muhammadu Buhari da gurguwar falsafar siyasa da mulkinsa da a ka k’udindino a matsayin chanji. Wannan chanji na Buhari, da a ka d’ora kwacankaf a kan caccakar na kan mulki ba tare da wasu takamemen ak’idodi da nagartattun tsare-tsare na mulki ba su ne su ka had’u da yak’in basasa na cikin gida a PDP su ka kada jam’iyyar.

Amma ni dai ko ba komai k’walliya ta kusan biyan kud’in sabulu, domin tabbas Lamido ya yi daidai da ya dawo da ni Jigawa na yi takara a 2015. Irin wad’annan zurfin tunani na Baba Lamido da mu ka amfana da shi ne ya sa da yawa ke kallon kamar biyayyar da mu ke yi masa ta wuce minsherin. Duk da na ta6a yin aikin likita a Jigawa na kusan tsawon shekara guda shekaru goma da su ka gabata a wancan lokacin, amma shafe sama da watanni biyar ana gudanar da yak’in neman zabe a dukkan lungu da sak’o na jihar ya k’aramin fahimta da kuma ba ni sani da k’wak’af a kan haqiqanin tattalin arzikinta, yanayin zamantakewar al’umma da al’adarta, inda siyasarmu ta dosa, da gungun matasan mu, yadda su ke kallon rayuwa, buk’atun su da kuma rauninsu, har ma da zahirin baranar da ke tunkarar muhallin jihar.

Duk da cewa an samu d’inbun nasarori a k’ok’arin magance wad’annan matsaloli a cikin shekara takwas na mulkin k’waf da k’waf irin na Lamido (alal misali, ni kai na mai rubuta wannan turancin, sheda ce ta irin matasa da a ka k’irk’ira a jihar duka a k’ok’arin mgance wad’ancan matsaloli); ina da k’wak’waran yak’inin cewa sai fa an juya akalar jihar kwacankaf kafin a dawwamar da ita a kan turba ta ci gaba mai d’orewa. Sai dai ni fa a wannan lokacin jiki na ya fara sanyi da siyasa irin ta takara. Amma duk da haka, jin ina da alhakin tallafawa a magance wasu matsalolin ya tursasa ni na samar da wasu tanade tanade na kashin kaina ta hanyar wata kafa mai zaman kan ta da kuma inganci ta ta6a alli domin samarwa da al’umma mafuta, da kuma wani zaure na ba da misali a aikace domin zaburar da al’umma; wato Gidauniyar Unik Impact (www.unikimpact.foundation) da kuma Gidan Rediyon Sawaba (sawabafm.com). Zan dawo kan waɗannan a gaba

Dalilai kusan uku ne ke sa mutane ganin kamar ina jan k’afa, d’ari-d’ari, tsoro, ko sanyin jiki a siyasa irin ta takara a Jihar Jigawa.

Na farko shi ne ban gama gamsuwa da wasu muhimman hanyoyin da ake amfani da su domin neman al’umma ba. Ni a iya abun da na gani yayi min kama da an d’ora tsarin kusan kwacankaf ne a kan turba mai kama da son rai, yaudara, da kuma a wasu lokutan, yanayi da kai tsaye yayi kama da ciniki, a maimakon wata tattaunawa zuzzurfa da k’ulla wata yarjejeniya domin samarwa ma fi akasari daga cikin al’umma mafita. Sai ma ya zama a na yi wa duk wani yunk’uri na irin wannan ingantattun hanyoyin na siyasa yarfe, da d’an k’ira, har ma da su jifa da sunaye irin; sabon yankan rake, ak’idar boko, ko kuma tunani irin na yara na yiwa duniya kallon fari da bak’i. Wannan shi ne dalilin da ya sa har kullum jiyan mu ke fin yau d’in mu k’yau. Dabara dai kuma ta rage ga mai shiga rijiya!

Dalili na biyu shine na kula cewa a galibi, ana kuskuren daukar gwagwarmayar siyasa a matsayin yunkurin y’an takara na k’ashin kan su domin gina kansu ta hanyar samawa kan su suna da kuma arzik’i, ba a matsayin gwagwarmayar had’aka domin fidda a’i daga rogo ba. Duk da ya ke za a iya cewa ma fi yawan y’an siyasar y’an neman sunnanne da kuma arzik’in, amma fa nauyi dai ya na nan a kan al’umma su zak’ulo k’alilan d’in da ba dole haka su ke ba. Rashin wayewa, talauci da yunwa su ne dalilan da a ka fi amfani da su wajen ba da uzurin wannan rashin sanin kan da kuma cinikantar da siyasar.

Toh, za a iya cewa hakanne. Domin idan a ka lura sosai za a ga cewa har yanzu kamar akwai 6ur6ushin tasarin mulukiyya na cewa ‘kowa ya tsaya a inda ya ke’ a cikin yanyin zamantakewar mu ta Musulmin arewa. Watak’ila wannan dalilin ya sa a ke hana Talakawa ilmi mai inganci, a ka kuma ci gaba da yiwa tattalin arzik’insu matsin kalangu ta hanyar rashin adalci kala-kala da aka jima ana shimfid’awa a wajen rabon arzik’in k’asa. Haka zalika da gaske ne cewar wasu daga cikinmu (ma su dama)na amfani da wannan jahilci da talaucin da aka ratayawa Mallam Talakan a wuya domin tabbatar da cewa ya ci gaba da wanzuwa a k’ark’ashin wannan kashin dankalin da aka yi masa. Amma fa ba anan kawai gizo ya ke sak’ar ba. Domin idan 6era na da sata toh tabbas daddawa ma fa na da warinta. Gaskiyar magana itace, idan mu ka yi tsam mu ka nazarci halayyar wasun mu Talakawan a wajen za6en shuwagabanni; kamar yanayin sai da k’uri’a, da za6e na son rai akan doron son zuciya, ko 6angaranci ba bisa ga cancanta ba, za mu iya yadda da cewar kamar shi Talakan ne da kansa ke bada kai bori ya hau. Saboda haka, ya zama wajibi a k’alubalanci shi kansa Talakan domin zaburar da shi ya shiga taitayinsa da kuma gwagwarmaya domin k’wato y’ancinsa da kuma samarwa da kansa sawaba a kan doro na fin k’arfin zuciyarsa.

Sai dalilina na uku, wadda kuma kamr ya fi dukka sauran tasiri. Wannan kuwa shine biyayya, jin nauyi, da k’ok’arin rik’e amanar tsohon Gwamna Sule Lamido, da kuma tabbatar da cewa ban bashi kunya ba, kai, har ma uwa uba da wani irin tauhidi da na sak’a duka a kan wannan doron.

A k’arshe dai duka wannan biyayyar, da jin nauyin da kuma shi kansa uwa uba d’an tauhidin na wa, da ma jan k’afar tawa a sisyasar gaba d’ayan su sai da a ka d’orasu a kan sahihin gwaji a bisa doron k’iraye-k’iraye na al’umma daban-daban na a zo a yi takara, da kuma sha’awar yin mulkin domin kawo irin gyaran da kullum mu ke magana a kansa, da kuma muradan gwagwarmayar neman k’ara k’warewa da gogayya a duniya.

Toh, lokaci alk’ali in ji bahaushe, domin kuwa a cikin shekarun nan goma, tsantsar tasirin abubuwan da ke turani, da kuma wadda ke rik’e ni a tsunduma harkar siyasa da kuma gwagwarmayar k’arin gogewa sun haifar da wani sakamako da kuma ilmi na musammnan, kai har ma da wasu yanayi ma su kamar tarar aradu da ka, da su ka tattaru su ka sa6a min kamanni; wasu da yawa a ak’idance, wasu kuma a danbarwar siyasa da zamantakewa a gida, kai har ma da wasu k’alilan a dai wannnan gwagwarmayar ta neman k’arin k’warewa da kuma gogayya a duniya.

Sai dai fa akwai d’inbun wahala, kuma tabbas jikina ya gaya min!!!

Zan ci gaba a wata ranar inshaAllah

Dr Nura..

Tsohon K’aramin Ministan Harkokin K’asashen Waje na Tarayyar Najeriya 2011-2015

Tsohon Ministan Yad’a Labarai na Tarayyar Najeriya 2014-2015

Toshon Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Jama’iyyar PDP a Jihar Jigawa 2015

Tsohon Dan Takarar Sanatan Jigawa ta Gabas na Jama’iyyar PDP 2023

Dalibin ‘Lafiya da Ci Gaban Duniya’ a University College da ke birnin London 2014 to date

Comments
Loading...