A Visionary Leader in Health and Public Service

Lissafi Ya Rikicewa ‘Yan Bokon Arewa…. (2)

0 10

Lissafi Ya Rikicewa ‘Yan Bokon Arewa…. (2)

A kashin farko na rubutu mai wannan take a sama, na yi k’ok’arin tambayar cewa toh shin shi kansa ‘Bokon’ ne ke da matsala”, ko kuwa irin ‘Bokon’ da aka mana ne mai matsalar, ko kuwa mu ‘yan ‘Bokon’ ne ba mu ma iya ‘Bokon’ ba?

Alhamdulillah, a cikin sama da mutum d’ari da su ka tofa albarkacin bakinsu, ku san babu wadda ya ce Bokon ne da kan sa ya ke da matsala. Amma fa an yiwa ‘yan Bokon ta k’ofar rago. A inda ma fi yawan tunanin masu tsokaci ya karkata ga mak’ala mana bak’in son zuciya da son kai. Kai wasu ma sun k’ara da cewa ‘yan Bokon ma gaba d’ayanmu hotiho ne. Ma’ana dai wai ta ginane kawai amma ba ta shiga ba. A tak’aice dai kawai ba mu ma iya bokon ba!!

Gaskiyar magana shine nima dai ku san hakan take; bi ma’ana shine, na yarda cewa;
“…Bokon da a ke koya mana ya na da matsala. Hakan ya sa sam sam ba mu ma iya bokon ba. Domin kuwa cikakken bokon ingattacce ba zai sa mutum irin bak’in son kai da mu ke fama da shi ba”

Son kai fa dabam, kuma bak’in son kai ma dabam. Son kai ku san halak ne. Kuma shine ma tushen wanzuwar ko wane jinsi na halitta (wato self preservation kenan a turance)

Amma shi kuwa bak’in son kai masiface a cikin al’umma. Irin wannan nau’in son kai shi ke sa bil adama bai ganin hagunsa bare damansa. Ya kuma sa mutum rufe ido, da toshe kunne, da kashe tunaninsa da k’wak’walwarsa a bisa duk wani abu da ya ji yana so a ransa. Shi fa wadda bak’in son kai ya tunzuro bai tunanin gobe ballantana jibinsa. A’ah, shi dai kawai ya samu biyan buk’atarsa ta yanzu yanzu. Duk abun da zai faru gobe kuwa ko ohonsa!

Shi dai bokon da bature mai jan kunne ya ke koyawa a chan k’asarsa a cike ya ke da dabarun;
‘Tunani mai zurfi duk kuwa rashin dad’insa (critical thinkin), da kuma hanyoyin warware matsalolin al’umma na yau da gobe (problem solving)’

Saboda dalilai na tarihi, da al’ada, da kuma son zuciya irin na Baturen, sai ya d’auke wad’ancan abubuwa biyu na sama daga cikin ilmin bokon da ya kawo mana shekaru ku san d’ari da su ka wuce. Mu dai iya bokon namu ya tsaya a karatu da rubutu da sanin nambobi (numeracy and literacy a turance). A tak’aice dai, mafiya yawan ‘yan bokon na mu fankam fankam ne ba funkaso ba!

Shi fa mai ingantaccen ilmi zai iya sanin cewa a duk lokacin da bak’in son ranka har ya 6ata duk wasu tsare tsare na tafikar da al’umma, toh kaima fa ba tsira za ka yi ba. A yau babu wani mahuluk’in da zai ce ya tsira daga halin tsaron da arewa ke ciki. Ko kuwa shi wannan azababben talaucin bai ganinsa a kusa da shi. Ko kuwa idan zuciyarsa ta buga zai iya samun ingattaccen taimakon gaggawa a cikin Nigeria

Toh don Allah ina amfanin bad’i ba rai?

Za mu ci gaba…

Comments
Loading...