Lissafi Ya Rikicewa ‘Yan Bokon Arewa… (1)
By Dr Nuruddeen Muhammad
Mutanenmu ‘yan boko, da alama fa wankin hula yana neman ya kai mu dare – ko ma in ce ya kai mu din!
Za a iya cewa tun kusan kimanin shekaru arba’in da biyar da suka wuce, wato a dai dai lokacin da aka rushe tsarin N. A. da ake amfani da shi a arewacin Najeriya a wancan lokaci, sannan aka maye gurbinsu da tsarin k’ananan hukomomi (Local Government Reform), ‘yan boko ne ke kid’ansu kuma suke rawarsu tun daga matakin gwamnatin tarayya, ya zuwa ga jahohi da kuma k’ananan hukomomi; idan ta yi k’yau su ne, in ma ba ta yi k’yau ba su din ne.
Gaskiyar magana ita ce, ba ta ma yi k’yan ba!
A hannunmu, mu ‘yan boko, ilmin al’umma ya sukurkuce, ya lalace. Haka zalika, a hannunmu al’amuran kiwon lafiya da tattalin arzik’in al’umma suka shiririce, suka balbalce. Tsaron K’asa da zaman lafiyarta, dukkansu a hannunmu su ka 6are. Aikin gwamnati kacokaf mu muka lalata abinmu. Siyasar ma sai mai kwali irin namu ne aka yarda ya yi takara ko da kuwa ta kansila ce, bare uwa uba takarar kujerar gwamna ko ta shugaban k’asa.
Mu ake nad’awa mukamai a matsayin kwamishinoni, da shuwagabannin ma’aikatun gwamnati na jihohi da na tarayya. Mu ne ministoci. Ko a lokacin mulkin soja, ai mune sojan kuma mune d’ansanda. Kuma har a yau d’innan, mune dai sojan kuma mune d’ansandan. Mu muke zama ‘yan majalisar dattijai kuma mune a ta wakilan. Mu ne lauyoyi kuma mune alk’alan. Mu ne malaman makaranta tun daga matakin firamare har zuwa jami’a. Mune likitoci, kuma mu ne asibiti.
Kai hatta ita kanta siyasar mu na da hannu dumu dumu a wajen wofantar da ita. Domin kuwa mune shuwagabannin hukumar za6e tun daga matakin k’asa har ya zuwa kan k’ananan hukomomi. Kuma mune ma’aikatan hukumar. Kai, mu ne ma ma’aikatan wuchingadi na za6e, kuma da mu ake rubuta sakamakon bogi, mu kuma sa hannu mu rantse akan cewa gaskiyace!
Amma fa ba wai ana nufin duka an taru an zamo daya ba ne. A’a, Allah ya gani akwai d’aid’aiku a cikin ‘yan bokonmu da su ka sadaukar da rayuwarsu wajen yin abin da ya dace a kowane irin hali da suka sami kansu a ciki. Sai dai gaskiyar magana ita ce, da yawa daga cikinmu da gangan kuma da niyya marar k’yau mu ka bari abubuwa suka tabarbare, suka koma yadda suke yanzu.
Hakan ya jawo zargi da rashin yarda suka shiga tsakanin al’ummarmu da kuma ‘yan bokonta, musamman ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati na kowane mataki. A yanzu dai kusan al’umma ta d’auki duk wani d’an siyasa a matsayin mai son zuciya – ko macuci, mayaudari. Ta kuma d’auki duk wani babban ma’aikacin gwamnati a matsayin d’an kore ko kuma d’an tokara a duk inda za a cuce su.
Toh kai mai karatu ya ka ke gani? Tunda kuwa ai dama Hausawa kan ce: mutumin da maciji ya sare shi, idan ya ga igiya gudu zai yi.
Sai dai fa a inda gizo ya ke sak’ar anan shine, idan dai ba sake tsarin mulkin k’asarnan aka yi ba, toh fa gyaran al’ummar nan dai dole ta kan tsarin siyasarnan da kuma ma su karatun bokon nan dai za a bi a samar da shi!
To, menene abin yi?
Shin ‘Bokon’ ne ke da matsala, ko kuwa irin ‘Bokon’ da aka koya mana ne mai matsalar, ko kuma ‘yan ‘Bokon’ ne ba su ma iya ‘Bokon’ ba?